Rundunar yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi bisa laifin kashe wani mutum bayan ya bi ta kansa da doki

0 63

Rundunar yan sandan Jihar Kano, ta kama wani Matashi dan shekara 18 mai suna Aminu Kabiru, bisa laifin kashe wani Mutum bayan ya bi ta kansa da Doki.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shine ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kano.

A cewarsa, lamarin ya faru ne jiya da misalin karfe 6:30 na Yamma a unguwar Gadon-Kaya, a lokacin da Marigayin ya dawo daga Kasuwa zuwa Gida.

Marigayin mai dan shekara 20 mai suna Abdulhadi Sammani, dan unguwar Sani-Mainagge ne ta Jihar Kano.

Sanarwar ta ce bayan hukumar yan sanda ta samu labarin faruwar lamarin, sun garzaya wurin, inda suka kaishi zuwa Asibitin Murtala Muhammad domin samun kulawar Likitoci.

SP Haruna Kiyawa, ya ce mutumin ya rasu a lokacin da Likitoci suke kulawa da shi, inda ya kara da cewa zasu gurfanar da mutumin a gaban Kotu domin girbar abinda ya shufa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: