CAN ta shawarci gwamntin tarayya ta kafa kwamatin Shugaban Kasa kan tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa

0 81

Kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN ta shawarci gwamntin tarayya ta kafa Kwamatin Shugaban Kasa kan tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa, tare da tsugunnar da mutanen da lamarin ya shafa.

Shugaban Kungiyar na Kasa Daniel Okoh, shine ya yi wannan kiran cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.

A cewarsa, kungiyar ta damu da yanayin da mutane ke ciki, a sanadiyar ambaliyar ruwa a kasar nan.

Kimanin mutane 500 ne aka bada rahotan mutuwar su, a sanadiyar abubuwa masu alaka ambaliyar, yayin da dubban mutane suka rabu da muhallan su.

Shugaban ya ce Kungiyar Kiristoci ta damu da halin da mutanen da ambaliyar ruwa ta raba da muhallan su da Gonakan su da kuma wuraren Ibadun su suke ciki.

Daniel Okoh, ya ce aikin Kwamatin Shugaban Kasa ya kamata ya kunshi neman taimakon kudade daga daidaikun mutane da kuma bangaren Gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, domin tallafawa mutanen.

Haka kuma ya yi kira kan a samar da Masalaha ta dindin domin kawo karshen matsalar ambaliyar ruwan a kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: