NEMA ta rabar da kayayyakin agaji ga sama da mutane 300,000 da ifti’la’in ya shafa a Najeriya

0 83

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Habibu Ahmed ya ce, gwamnatin tarayya ta samar da kayayyakin agaji ga sama da mutane 300,000 da ifiti’i ya shafa a fadin kasar nan.

Ahmed wanda ya bayyana hakan a karshen makon da ya gabata yayin da yake gabatar da kayan abinci ga gwamnatin jihar Sokoto domin cigaba da rabawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da marasa galihu a jihar.

Ya ce sunkai  kayayyakin ne domin tallafawa masu karamin karfi a jihar.

Babban daraktan ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta kafa kwamitocin bada agajin gaggawa na kananan hukumomi a dukkanin kananan hukumomi 23.

Ya kara da cewa ya kamata a ware kudaden da za a iya amfani dasu wajen tantance irin iftila’in daya shafi.

Sakataren gwamnatin jihar Mainasara Ahmed, ya godewa gwamnatin tarayya bisa wannan tallafin tare da bada tabbacin cewa za’a raba kayayyakin cikin adalci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: