Jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da manufar rufe iyakokin Najeriya da shugaban kasa Buhari ya yi

0 75

Jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da manufar rufe iyakokin kasar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi..

Shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Jigawa, Alhaji Isa Duniya Bahutu ne, ya bayyana hakan jiya a taron tuntubar jam’iyyar PDP da aka gudanar a karamar hukumar Yankwashi.

Ya zargi jami’an kwastam da laifin kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, sakamakon sintiri na baya-bayan nan a kan iyakar Babura da Jamhuriyyar Nijar.

Ya yi kira ga masu kada kuri’a akan su koya wa jam’iyyar APC darasi na siyasa ta hanyar kin amincewa da ita a zaben 2023.

Tun da farko dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Alhaji Mustapha Sule Lamido ya zargi gwamnatin jihar Jigawa da cire tsofaffi daga dukkanin ayyukan kiwon lafiya na jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: