Akwai dalilan da yasa na ki halartar shirin da kwamitin hadin gwiwa na Arewa ya shirya wa ‘yan takarar shugabancin kasa

0 97

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Kwankwaso ya ki amsa gayyatar da aka yi masa na halartar wani shiri da kwamitin hadin gwiwa na Arewa ya shirya wa ‘yan takarar shugabancin kasa.

Kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Abdulmumini Jibrin Kofa, a wata wasika mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Oktoba, 2022, ya ce sun yanke shawarar ne saboda sun gano cewa kwamitin ya shirya nuna wani ne a matsayin dan takarar da suke so mutanen Arewa su zaba.

Kwamitin wanda ya hada da kungiyar Arewa Consultative Forum, Arewa Elders Forum, Sir Ahmadu Bello Foundation, Arewa Research and Development Project, da Jamiyyar Matan Arewa.

Sun gayyaci wasu ‘yan takarar shugabancin kasa domin yin wani taron tattaunawa a Kaduna.

Shirin wanda aka fara a jiya, ya samu halartar dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da Kola Abiola na jam’iyyar PRP, da Adewale Adeboye na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).

A yau ne ake sa ran dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar (APC) Bola Tinubu da Peter Obi na jam’iyyar Labour Party da kuma dan takarar jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso za su halarci taron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: