Saboda yada tarukan siyasar dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP gwamnatin jihar zamfara ta rufe tashoshi guda 5

0 56

Hukumar dake kula da kafafen yada labarai ta kasa, NBC, ta zargi gwamnatin jihar Zamfara da rufe wasu kafafen yada labarai guda hudu a jihar ba bisa ka’ida ba.

Kafin hakan dai Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa a jiya ne gwamnatin jihar Zamfara ta rufe ofisoshin NTA, Pride FM, Gamji TV da kuma Al’umma TV a jihar.

Saboda yada tarukan siyasar dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Dauda Lawal.

Kwamishinan yada labarai na jihar Ibrahim Dosara ne ya sanar da hakan a gidan rediyon jihar.

Sai dai wata sanarwa da babban daraktan hukumar yada labarai ta kasa, Balarabe Illela ya fitar.

Ya bukaci gwamnatin jihar ta janye matakin, yana mai cewa tuni hukumar ta ja hankalin gwamnati kan rashin bin doka da oda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: