‘Kokarin gwamna Badaru wajen farfado da ilimin jihar Jigawa ne yasa muka karramashi’ a cewar Kungiyar Dalibai ta Kasa

0 93

Kungiyar dalibai ta kasa NANS ta bada lambar yabo ga Gwamna Mohammed Badaru Abubakar bisa nasarorin da ya samu a fannin Ilimi.

Shugaban kungiyar na kasa, Comrade Usman Barambu wanda ya mika lambar yabon ga gwamnan, ya bayyana nasarorin da gwamna ya samu a bangaren ilimi da cewar suna da ban mamaki.

Ya kara da cewa Gwamna Badaru Abubakar na daga ciki

gwamnanonin kasar nan da ya yi fice wajen ba da fifiko ga ilimi.

Comrade Usman yana mai cewar sun bashi lambar yabon ne domin yin godiya ga gwamnan kan kokarinsa na bunkasa harkokin ilmi.

Hakazalika kungiyar ta mika katin murnar cikar gwamnan shekaru 60 da haihuwa.

A nasa jawabin, gwamna Badaru Abubakar ya yabawa kungiyar da kuma shugaban ta na kasa bisa wannan karamci.

Inda ya shawarce su dasu kara maida hankali kan karatunsu tare da sauya tsarin tafiyar da harkokin kungiyar domin kara mata farin jini da kuma arkashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: