Adadin fursunoni dubu 3 da 906 ne suka tsere daga gidajen gyaran da’a har yanzu kuma ba a kama su ba

0 91

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa adadin fursunoni dubu 3 da 906 da suka tsere daga gidajen gyaran da’a a kasar har yanzu ba a kama su ba.

Aregbesola ya bayyana hakan ne a yau a yayin wani taron manema labarai da tawagar manema labarai ta shugaban kasa ta shirya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ministan ya ce adadin fursunoni dubu 4 da 369 ne suka tsere daga gidajen yarin daga bara zuwa yau.

Yace daga cikin wannan adadin an sake kama 984.

Aregbesola ya kuma ce fursunoni 465 ne ke gudanar da digiri daban-daban a fadin kasarnan, inda ya ce 85 daga ciki suna gudanar da shirye-shiryen karatun digiri na biyu ciki har da 4 da ke yin karatun digirin digir-gir.

Yace fursunoni 560 ne suka shiga jarabawar WAEC/NECO yayin da dubu 2 da 300 suka yi rijistar karatun manya a gidajen yari da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: