Shugaba Buhari a birnin Paris ya gana da shugaban bankin cigaban addinin musulunci inda ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatinsa ta himmatu wajen inganta ayyukan gine-gine

0 105

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yau a birnin Paris na kasar Faransa ya gana da shugaban bankin cigaban addinin musulunci Dr Mohammed Al-Jasser inda ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatinsa ta himmatu wajen inganta ayyukan gine-gine.

Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina, a wata sanarwa da ya fitar ya ce an gudanar da taron ne a gefen taron zaman lafiya na birnin Paris.

Shugaban kasar ya godewa bankin cigaban Musulunci da taimakon da ya bayar ya zuwa yanzu, inda ya ce abin da Najeriya ta dogara da shi wato danyen mai, darajarsa na raguwa.

A nasa jawabin, Al-Jasser ya ce ya yi farin cikin ganin irin hadin gwiwa tsakanin Najeriya da bankin cigaban Musulunci tun bayan da ya fara aiki watanni uku da suka gabata.

Shugaban bankin na cigaban Musulunci ya ce babban aikin bankin shi ne inganta cigaba a tsakanin masu ruwa da tsaki, kuma zai cigaba da baiwa Najeriya hadin kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: