Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu kuma farar fata na karshe da ya jagoranci kasar ya rasu yana da shekaru 85

0 83

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu kuma farar fata na karshe da ya jagoranci kasar Federick William de Klerk ya rasu yana da shekaru 85 a duniya.

De Klerk, wanda shi ma ya kasance jigo a fagen sauyin mulki zuwa dimokuradiyya, an gano cewa ya kamu da cutar daji a bana.

Ya kasance shugaban kasa tsakanin watan Satumbar 1989 zuwa Mayun 1994.

A shekarar 1990, ya bayar da umarnin a saki Nelson Mandela daga gidan yari, wanda ya kai ga gudanar da zabe mai cike da tarihi da ya kai shugaban masu adawa da wariyar launin fata kan karagar mulki.

De Klerk ya raba lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel tare da Mandela saboda taimakawa wajen yin shawarwarin kawo karshen wariyar launin fata.

A wata sanarwa da gidauniyar De Klerk ta tsohon shugaban kasar ta fitar a yau ta ce ya rasu ne a gidansa da ke birnin Cape Town cikin kwanciyar hankali sakamakon ciwon daji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: