Masanin cututtuka na jihar, Dakta Msuega Asema, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, lokacin da kwamishinan lafiya da jin daɗin jama’a na jihar, Dakta Paul Ejeh-Ogwuche, ya kai ziyara cibiyoyin killace marasa lafiya da ke asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Benue da ke Makurdi da kuma cibiyar lafiya ta tarayya da ke Apir, inda ake kula da waɗanda suka kamu da cutar.
Tun da farko a watan nan ne kwamishinan ya ayyana bullar cutar a hukumance, bayan samun ƙarin waɗanda ake zargi sun kamu. A ranar 16 ga Fabrairu, ya shaida wa manema labarai cewa ma’aikatan lafiya huɗu sun rasa rayukansu, yayin da sama da mutane 60 ake zargin sun kamu.
Sai dai yayin ziyarar tantance halin da ake ciki a asibitocin, Dakta Asema ya ce jihar na fuskantar ɓarkewar cutar, inda aka tabbatar da mutane 45 sun kamu, kuma jimillar mace-mace ta kai 10 cikin mutum 250 da ake zargi sun kamu.
Ya ce alkaluman sun haɗa da ma’aikatan lafiya da dama, ciki har da likitoci biyar, nas-nas huɗu, ma’aikatan jinya na al’umma biyu da kuma ma’aikacin lafiya guda ɗaya.
Kwamishinan lafiya ya roƙi jama’a da kada su firgita da alkaluman, yana mai cewa gwamnati na ƙara zage dantse domin dakile cutar tun bayan ayyana ɓarkewarta a ranar 3 ga Fabrairu.
Ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna goyon baya ga marasa lafiyar da ke karɓar magani, tare da duba yadda cibiyoyin ke aiki domin ƙara inganta matakan dakile cutar, musamman ganin cewa ana samun yaɗuwar ta daga mutum zuwa mutum sakamakon gibi a matakan kariya.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ƙarƙashin gwamna Hyacinth Alia ta himmatu wajen ganin an shawo kan lamarin cikin gaggawa. Ya ce an tura jami’an sa ido a kan cututtuka zuwa ƙananan hukumomi 23 na jihar domin ƙarfafa bibiyar waɗanda suka yi mu’amala da masu cutar da kuma wayar da kan al’umma.
Haka kuma ya buƙaci duk wanda ya ga alamun cutar da ya garzaya cibiyoyin lafiya domin a gano cutar da wuri, yana mai jaddada cewa gano cutar cikin lokaci na rage mace-mace.
Ya kuma yaba wa ma’aikatan lafiya kan jajircewarsu, tare da jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu.
A nasa ɓangaren, babban daraktan asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Benue da ke Makurdi, Dakta Stephen Hwande, ya ce asibitin ya ɗauki matakai masu ƙarfi domin dakile cutar, yana mai kira ga mazauna jihar da su bi ƙa’idojin kariya daga kamuwa da cututtuka.
Shi ma babban daraktan cibiyar lafiya ta tarayya da ke Apir, Farfesa Joseph Kontor, ta bakin wakilinsa Dakta Uche Augustine Azuka, ya ce dakin gwaje-gwajen cibiyar na gudanar da bincike kan cututtuka daban-daban ciki har da zazzabin Lassa, amma rashin wutar lantarki na kawo cikas ga ayyukansu.
Ya roƙi gwamnatin jihar da ta taimaka wajen samar da wutar lantarki da kayan kariya ga ma’aikata, yana mai cewa ana kula da marasa lafiya tare da sallamarsu ba tare da karɓar kuɗi ba.