Ado Doguwa ya yi nasara a kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a Kano

0 215

Tsohon Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya yi nasara a karar da Salisu Yushau Abdullahi na jam’iyyar NNPP ya shigar a gaban kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a Kano.

Tun da farko dai Abdullahi na jam’iyyar NNPP ya roki kotun da ta soke nasarar Alhassan Doguwa a matsayin wakilin mazabar Doguwa da Tudun Wada a Majalisar Tarayya.

Sai dai da yake yanke hukunci kan karar da Abdullahi ya shigar a kan dan takarar na jam’iyyar APC, kwamitin alkalan mai mutum uku karkashin jagorancin mai shari’a L.B. Owolabi ya ce wanda ya shigar da karar ya gaza tabbatar da kokensa da gamsassun hujjoji kamar yadda doka ta tanada.

Mai shari’a Owolabi ya ce duk dalilai uku da mai karar ya dogara da su  da suka hada da cin hanci da rashawa da Doguwa ya yi, da rashin samun halastattun kuri’un da ake bukata ba su da tushe balle makama.

Kotun, a cikin hukuncin da ta yanke, ta amince da cewa dukkan shaidu 32 da mai kara ya gabatar, sun kasa bayar da kwakkwarar hujjar da za ta tilasta a soke zaben. Hukumar zaben ta bayyana Doguwa a matsyin wanda ya lashe zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: