Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta amince da kafa Asusun jin kai don yaki da Talauci

0 176

A wani labarin kuma Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta amince da kafa Asusun jin kai don yaki da Talauci.

Ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da manema labaran fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala zaman majalissar jiya Litinin a Abuja.

Ta ce an amince da asusun ne don baiwa Gwamnatin Tarayya damar bada tallafi a kasar nan.

A cewarta, Gwamnatin Tarayya na fatan tara akalla dala biliyan 5 a duk shekara a cikin asusun don tallafawa yan kasa.

Edu ta bayyana cewa za a samu kudaden ne daga gwamnatin tarayya, da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma kungiyoyin  kasa da kasa da sauran masu hannu da shuni.

Ta kuma ba da tabbacin cewa za a gudanar da ayyukan a dukkan jihohin kasar nan 37 da babban birinin tarayya Abuja.

Ministar ta ce majalissar ta dauki matakin amincewa da yarjejeniyar kare hakkin tsofaffi a kasar kamar yadda kundin tsarin mulkin ya tanada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: