Akalla Mutane 288 Ne Suka Mutu A Wani Hatsarin Taho Mugama Da Wasu Jiragen Kasa 3 Suka Yi A Indiya

Akalla mutane 288 ne suka mutu yayin da daruruwa suka jikkata a wani hatsarin taho mugama da wasu jiragen kasa 3 suka yi a Indiya, a wani hatsarin jirgin kasa mafi muni cikin shekaru 20.
Hatsarin wanda ya auku yankin Balasore dake gabashin jihar Odisha, inda wasu sassan jirgin suka fallatsa zuwa gefen titin.
An ga yadda Jini ya Malala a cikin wasu daga cikin taragon jirgin a cikin daren jiya lokacin da masu aikin ceto suka isa wajen.
Wani daga cikin wadanda suka tsalleke Rijiya da baya a hatsarin ya gayawa gidan talabijin na Bengali cewa sun ga mutane suna tashi sama bayan wata karar aradu. Hatsarin ya auku ne a dai-dai Babbar mahadar hanyar jirgin data arewacin kasar da kuma Bengaluru zuwa Kolkata.