Akalla mutane takwas ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Zacholi da ke arewa maso gabashin kasar Ghana

0 19

Akalla mutane takwas ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Zacholi da ke arewa maso gabashin kasar Ghana.

An kuma lalata wasu gidaje a harin.

Rundunar ‘yan sandan kasar ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin.

Ba a dai san dalilin maharan ba, amma yankin na fuskantar matsalolin tsaro da suka hada da fashi da makami da rikicin kabilanci.

Harin ya faru ne mako guda bayan da ministan tsaron Ghana ya ce an kara matakan tsaro saboda yiyuwar abin da ya kira hare-haren ta’addanci.

Harin ba zai rasa nasaba ba da munanan tashe-tashen hankulan da ‘yan bindiga ke haddasawa a kasashe makwabta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: