Labarai

Jami’an ‘yan sanda hudu ne suka mutu yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wata helkwatar ‘yan sanda ta jihar Anambra

Jami’an ‘yan sanda hudu ne suka mutu a jiya yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a helkwatar ‘yan sanda reshen Atani dake karamar hukumar Ogbaru a jihar Anambra.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Echeng Echeng ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya.

Tochukwu Ikenga ya ce abin takaici ne yadda aka kashe jami’an ‘yan sanda hudu, yayin artabu da bindiga.

Kakakin ‘yan sandan ya ce daukin gaggawar da jami’an ‘yan sandan suka kai ne ya ceci ginin daga harin ‘yan bindigar.

Tochukwu Ikenga ya ce ‘yan sanda sun fara tattara bayanan sirri domin zakulo wadanda ake zargi da kai harin.

Harin na baya-bayan nan na zuwa ne kasa da mako guda bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a helkwatar karamar hukumar Aguata da ke jihar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: