Wata mahaukaciyar guguwar ruwan sama ta lalata gidaje da dama na miliyoyin naira a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ruwan sama na farko a bana wanda aka kwarara kamar da bakin kwarya, ya fara zuba ‘yan mintoci kadan bayan karfe 3 na yammacin ranar Talata kuma ya dauki sama da sa’o’i hudu.

Ruwan saman ya lalata gidaje da dama na kasa a wasu sassa na tsakiyar birnin, inda ya raba mutane da dama da gidajensu.

‘Yan jaridan da suka zagaya cikin babban birnin sun lura cewa guguwar ta lalata rufin gidaje da dama tare da tumbuke itatuwa a wurare da dama a cikin birnin Maiduguri da kewaye, lamarin da ya tilastawa jama’a kwashe tarkace da datti da sauran kayayyakin da guguwar ta lalata.

Duk kokarin jin ta bakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno ya ci tura, amma wasu ma’aikatan hukumar da ba su so a bayyana sunayensu ba sun ce jami’an hukumar sun fara tantance barnar da guguwar ta yi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: