Labarai

Akalla ‘yan takarar jam’iyyar APC 104 ne ke fafatukar neman tikitin jam’iyyar na neman kujeru 30 a majalisar dokokin jihar Jigawa

akalla ‘yan APC 104 ne ke fafatukar neman tikitin jam’iyyar na neman kujeru 30 a majalisar dokokin jihar Jigawa.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Aminu Sani Gumel ne ya bayyana haka.

Aminu Sani ya lura cewa, babu wata mace ko daya da ta nuna sha’awar kujerar majalisar dokokin jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya bayar da rahoton cewa, ‘yan takara 104 da ke neman kujerun majalisar dokokin jihar sun hada da masu neman tazarce da kuma wadanda ke neman kujerun a karon farko.

Shugabar matan jam’iyyar APC a jihar, Hajiya Dayyaba Shuaibu, ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran cewa, a baya wasu mata uku sun nuna sha’awarsu ta tsayawa takarar.

Ta ce har an umurci matan da su tuntubi shugabannin mazabunsu da kuma shugaban jam’iyyar na jiha dangane da burinsu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: