Wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan kungiyar ‘yan banga hudu a Awka, babban birnin jihar Anambra.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 da rabi na yamma.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, a wata sanarwa da ya fitar a yau, ya ce ‘yan sanda sun mayar da martani kan harin da aka kai wa ‘yan banga.

Kakakin ‘yan sandan ya ce an yi artabu tsakanin ‘yan bindigar da jami’an ‘yan sandan da suka amsa kiran gaggawa.

Kakakin ‘yan sandan ya ce, a wani lamari na daban, ‘yan sandan sun ceto wani da aka yi garkuwa da shi.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga biyar ne suka sace mutumin a makon da ya gabata inda daga bisani suka bukaci a biya naira miliyan 10 na kudin fansa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: