Al’ummar Idomaland Sun Yanke Shawarar Tura Babbar Tawaga Zuwa Ga Shugaba Buhari

0 101

Biyo bayan hare-haren da makiyaya suka kai kan wasu al’ummar yankin mazabar Benuwe ta Kudu da aka fi sani da Idomaland ‘ya’ya maza da mata na al’ummar kasar nan sun yanke shawarar tura wata babbar tawaga zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A cewar sanarwar da mai taimaka wa sarkin kan harkokin yada labarai, Onuminya Odoba ya rabawa manema labarai, shugaban majalisar gargajiya na yankin Idoma, Ochidoma, Mai Martaba, John Elaigwu ne ya kira taron.
Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai hari a kauyukan Igbobi da Umogidi a kananan hukumomin Apa da Otukpo a yankin Idomaland, inda aka ce an kashe mutane akalla 56 cikin kwanaki uku.
Taron ya yanke shawarar kafa wani dandali na Idoma Local Orientation Platform don zaburar da shirin hadin kan Idoma, musamman ta hanyar zane-zane da kasidu bayan lura da wajibcin tsayawa tsayin daka a kan dalilansu na bai daya da kuma koyi zama da hadin kai tare da fahimtar ainihin ‘yan uwantaka. hadin kai, soyayya, adalci, da daidaito.

Leave a Reply

%d bloggers like this: