Ambaliyar ruwa ta mamaye garin Bindigi da ke jihar Yobe

0 158

Rahotanni daga jihar Yobe, na cewa ambaliyar ruwa ta mamaye garin Bindigi da ke karamar hukumar Fune inda ta lalata gidaje akalla 50, da gonaki.

Kazalika ambaliyar ta kuma yi awon gaba da dabbobi da dama.

Tuni dai mutanen garin da dama da ambaliyar ta afkawa suka koma wata makaranta da asibiti inda suka samu mafaka.

Yanzu haka dai jama’ar garin na Bindigi na can cikin halin kaka-nika-yi sakamakon afkuwar ambaliyar ruwan da ta mamaye garin.

Wani mazaunin garin da BBC ta tattauna da shi ta wayar tarho, Bulama Alhaji Audu, ya ce ambaliyar ruwan ta wuce yadda ake tsammani.

A nata ɓangaren, gwamnatin jihar ta Yobe ta ce tana kokarin kai daukin gaggawa garin da ma sauran wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Dakta Muhammad Goje, shi ne shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ya shaida wa BBC cewa, ko shakka babu sun samu labarin abin da ya afku na ambaliya, ba a Bindigi kadai ba har ma da wasu wurare.

Gwamnatin tarayyar Najeriya dai ta yi hasashen cewa za a samu mamakon ruwan sama a kwana biyar masu zuwa kuma zai iya janyo ambaliyar ruwa a wurare 123 na jihohi 21 na ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: