Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kudirin kara kasafin kudin jihar da naira biliyan 99.2

0 89

Kudirin ya samu karbuwa daga dukkan kwamitin majalisar baki daya bayan kammala karatu na uku a zauren majalisar a ranar Alhamis.

Gwamna Abba Yusuf ya gabatar da kudirin dokar ne a ranar 26 ga Agusta, 2024 inda ya nemi a kara kasafin kudin. 

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala zaman majalisar, shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Hon. Aminu Sa’ad, ya bayyana cewa, kashi 58 cikin 100 na kasafin kudin an ware su ne domin manyan ayyuka na more rayuwa yayin da kashi 42 cikin 100 kuma aka ware domin gudanar da ayyukan yau da kullum.

Hon. Sa’ad ya kara da cewa, karin kasafin kudin an yi shi ne domin aiwatar da zabukan kananan hukumomi da ke tafe, biyan sabon mafi karancin albashi, kudaden gudanarwa a sabbin ma’aikatun da aka kafa da sake bude cibiyoyin koyar da sana’o’i da sauran ayyukan da gwamnati ta sa gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: