An bukaci gwamnatin tarayya da ta kawo karshen ta’addanci a Najeriya

0 106

Kungiyar Hadin Kan Addinai ta kasa (NIREC) ta bukaci gwamnatin tarayya da ta kawo karshen ta’addanci da kashe-kashe da sace-sace da kuma fashi da makami da aka yi a kasar cikin makon jiya.

A wata sanarwa da Kungiyar ta fitar jiya a karkashin jagorancin shugaban kungiyar kiristoci ta kasa (CAN), Daniel Okoh, da mai alfarma Sarkin Musulmi, wanda ya zama shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci NSCIA. Alhaji Sa’ad Abubakar.

Majalisar hadin gwiwar ta ce ta damu matuka dangane da karuwar rashin tsaro da ake fama da shi a fadin kasar.

Majalisar addinan ta jajantawa iyalan duk wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan aika-aika, tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu sanna Allah bawa wadanda suka samu raunuka lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: