Mutane 5 sun nutse cikin ruwa a jihar Jigawa

0 360

Akalla mutane biyar ne aka ruwaito sun nutse a ruwa a garin Gantsa, hedikwatar karamar hukumar Buji a jihar Jigawa.

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawal Shiisu Adams ya fitar, ya kuma rabawa manema labarai.

Sanarwar ta kara da cewa, a jiya Talata, ‘yan sanda a garin Gantsa sun samu labarin cewa mutane biyar sun nutse a cikin garin. 

Daga bisani an kai su Asibitin Gantsa Cottage, inda Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwar dukkansu.

Sanarwar ta kara da cewa, daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su akwai yara biyu masu shekaru biyu da shekaru bakwai da kuma wata yarinya Fiddausi Dahiru da Lurwanu Adamu mai shekaru 30 da kuma Idris Abubakar mai shekaru 50. 

An mika gawarwakin ga ‘yan uwansu domin yi musu jana’iza.

Idan ba a manta ba a makonnin da suka gabata wasu ‘yan mata uku su ma sun nutse tare da rasa rayukansu a wani tafki a kauyen Tulla da ke karamar hukumar Buji. 

Bugu da kari, mutane biyu, uba da da, sun mutu a cikin mako guda lokacin da gidansu ya rufta sakamakon ruwan sama mai karfi da ya haddasa ambaliya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: