Hukumomin USAID da PfD sun mika ingantattun kayayyakin tsaftar muhalli ga jihohin Kano da Jigawa

0 103

Hukumar Raya Kasa da Kasa ta Amurka (USAID) da abokan huldar ci gaba (PfD), sun mika ingantattun kayayyakin ruwa da tsaftar muhalli ga jihohin Kano da Jigawa.

An aiwatar da ayyukan ta hanyar inganta ruwa da haɓaka tsaftar ruwa (WISE) (USAID/PfD) daga Agusta 2021 zuwa Agusta 2024.

Makasudin gudanar da ayyukan shi ne rage yaduwar cutattukan da ruwa ke janyowa a tsakanin al’umma, musamman kananan yara da mata da tsofaffi da ba su da basu kariya a jihohin Jigawa da Kano.

Har ila yau, ayyukan, sun ba da horo ga masu sana’a don gina rijiyoyin burtsatse da kuma wuraren wanka, tare da tallafa wa gidaje sama da 12,000 don gina wuraren wanka da sauran su.

Bayanai sun nuna cewa, an samar da ingantattun wuraren samar da ruwa guda 55 a garin Miga da Kaugama a jihar Jigawa yayin samar da 43 a girka a kananan hukumomin Gezawa da Karaye na jihar Kano.

Kwamishinan Raya Karkara na Jihar Kano Abbas Sani Abbas ne ya bayyana kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da dorewa aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: