An Fallasa Jagoran ’Yan Ta’addan da Ke da Hannu A Mummunan Kisan Kiyashin Kwara

0 176

Kisan gillar da ya faru a ranar Talata a ƙauyen Woro, da ke ƙaramar hukumar Kaiama a Jihar Kwara, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 176, ba hatsari ba ne kawai, sai dai wani shiri ne da aka tsara tun tuni, wanda ke nuna faɗaɗar ayyukan ’yan ta’adda zuwa yankin Arewa ta Tsakiya.

Binciken jaridar Saturday PUNCH ya nuna cewa harin ya samo asali ne daga gazawar hukumomin tsaro wajen dakile gargaɗin da aka samu tun kafin aukuwar lamarin, inda ake zargin wani babban kwamandan ’yan ta’adda mai suna Abubakar Saidu, wanda aka fi sani da Sadiku, a matsayin jagoran harin.

Rahotanni sun bayyana cewa Sadiku ya shafe sama da shekara 12 yana aikata ta’addanci, inda ya fara ne a matsayin amintaccen mataimaki ga marigayi shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, kafin daga bisani ya koma abin da masana tsaro ke kira “Shekau na Arewa ta Tsakiya” zuwa shekarar 2026.

Bayan matsin lambar sojoji ya raunana Boko Haram a Arewa maso Gabas, Sadiku ya koma yankunan dazuzzuka na jihohin Niger da Kwara, musamman dajin Kainji, inda ya kafa sansanoni tare da ƙaddamar da hare-hare da suka lalata rayuwar manoma, tilasta wa dubban jama’a gudun hijira, tare da haddasa mummunan kisan kiyashi a Woro.

Masana tsaro sun bayyana dajin Kainji a matsayin “sabuwar Sambisa”, saboda yadda yake zama mafaka ga ’yan ta’adda daga Arewa maso Gabas da kuma ragowar ’yan fashi daga Arewa maso Yamma, inda ake amfani da shi wajen ɗaukar mayaƙa, safarar makamai da kai hare-hare a jihohi da dama.

Shaidun da suka tsira daga harin sun ce maharan sun mamaye Woro ne da yamma, inda suka hau kan babura dauke da muggan makamai, suka kewaye ƙauyen, tare da rufe hanyoyin fita, inda suka fara kisan gilla daga gida zuwa gida, ciki har da kona fadar sarkin gari da sace mata da yara.

 Duk da cewa an ce an sanar da hukumomi tun makonni kafin harin, rahotanni sun nuna cewa sojoji sun isa yankin ne bayan awanni kusan goma, inda ’yan ta’addan suka riga suka tsere, lamarin da ya sake jefa tambaya kan shirye-shiryen tsaro da kuma buƙatar gyaran tsarin tsaron Najeriya baki ɗaya.

Leave a Reply