’Yan Ta’adda Sun Sake Kai Hari  Benue, Sun Kashe Mutane 13 Kwanaki Kaɗan Bayan Harin Baya

0 362

Ana zargin wasu ’yan ta’adda da sake komawa Ƙaramar Hukumar Kwande da ke Jihar Benue, inda suka kashe aƙalla mutane 13 a wani sabon hari da suka kai kasuwar Anwase da ke yankin Mbaikyor.

Harin ya faru ne a ranar Juma’a a kasuwar da ke cike da jama’a, kwanaki kaɗan bayan harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a ƙauyen Abande da ke ƙaramar hukumar.

 Rahotanni sun ce maharan sun buɗe wuta kan ’yan kasuwa da mazauna yankin, tare da sace wasu mata yan kasuwa, sannan suka ƙone shaguna da rumfunan kasuwa.

Wani mataimaki ga shugaban ƙaramar hukumar Kwande, Ibi Andrew, ya tabbatar wa Channels TV cewa mutane 13 ne suka mutu, inda ya ce shugaban ƙaramar hukumar, Vitalis Neji, tare da jami’an tsaro sun garzaya yankin domin daƙile tashin hankalin.

Shaidu sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun fito ne daga wani dutse da ke kusa da kasuwar, inda suka riƙa harbi ba kakkautawa, lamarin da ya jefa ’yan kasuwa da masu sayayya cikin firgici tare da tserewa domin tsira da rayukansu.

Mazauna yankin sun ce an sace mata da dama yayin harin, yayin da iyalai ke ci gaba da neman ’yan uwansu da suka ɓace, sai dai kakakin rundunar ’yan sandan jihar Benue bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka aika masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Wannan sabon hari ya ƙara tsananta matsalar tsaro a Kwande da ma Jihar Benue gaba ɗaya, inda mazauna yankin ke kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa domin dakatar da kashe-kashen da ke ci gaba da addabar al’ummah..

Leave a Reply