Matashi A Jahar Kano Ya Rasa Ransa Sanadiyyar Nutse Wa A Ruwa

0 185

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Yusif Malam-Gwani ya rasu bayan da ya nutse a wani ruwa da ke unguwar Bachirawa, Kwanar Madugu, a Karamar Hukumar Ungogo.

Darakta Janar na hukumar, Sani Anas, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis a Kano.

Ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa daga wani mutum mai suna Sulaiman Abdullahi-Tela da yammacin ranar Alhamis, yana sanar da cewa matashin ya faɗa cikin ruwan.

Bayan samun rahoton, Abdullahi ya ce nan take aka tura tawagar ceto daga hedikwatar hukumar zuwa wurin da lamarin ya faru domin ɗaukar matakin gaggawa.

Sai dai bayan an fitar da matashin daga cikin ruwan, an tabbatar da cewa ya riga ya rasu, inda aka miƙa gawarsa ga dagacin unguwar Bachirawa, Jibrin Isah.

A wani lamari na daban, hukumar ta ce wani yaro ɗan shekara takwas mai suna Abdussalam Ibrahim shi ma ya faɗa cikin wata rijiya a yankin Kofar Yamma, cikin garin Karaye na Karamar Hukumar Karaye.

Hukumar ta ce an fitar da yaron daga rijiyar amma ya rasu, inda aka miƙa gawarsa ga mahaifinsa, Malam Musa-Mudi, tare da kira ga al’umma da su ƙara kula da rijiyoyi da wuraren ruwa, musamman domin kare rayukan yara, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan.

Leave a Reply