Amurka Ta Yi Allah-Wadai da Kisan Gillar da Aka Yi Wa Al’umma A Kwara, Ta Kuma Goyi Bayan Tura Jami’an Soja

0 183

Amurka ta yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa al’umma a Karamar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce kan adadin mutanen da suka rasa rayukansu tare da tayar da hankalin jama’a a Najeriya da ma ƙasashen duniya.

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ce mutane 75 ne aka tabbatar sun mutu a hare-haren da aka kai a ƙauyukan Woro da Nuku, sai dai rahotanni daga mazauna yankin da kuma wasu masu sa ido na ƙasashen waje sun nuna cewa adadin ya fi haka nesa ba kusa.

A wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a shafin X ranar Juma’a, ya bayyana harin a matsayin abin firgici, inda ya ce ana fargabar cewa sama da mutane 160 ne suka mutu, yayin da har yanzu ba a san makomar wasu da dama ba.

Sanarwar ta ce Amurka na mika ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa, tana mai bayyana harin a matsayin tashin hankali marar misaltuwa da ya girgiza zukatan al’umma.

Haka kuma Amurka ta yaba da umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar na tura jami’an tsaro domin kare ƙauyukan da abin ya shafa, tare da umartar hukumomin tarayya da na jihohi da su tallafa wa mutanen yankin da kuma kamo masu hannu a wannan aika-aika.

Martanin na Amurka ya ƙara jaddada yadda kasashen duniya sukayi tir da harin, ciki kuwa harda Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƙasar Turkiyya

Tun da farko, Shugaba Tinubu ya amince da tura bataliya soji zuwa Kaiama tare da kafa sabon sansanin soja, yayin da Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, suka tabbatar da cewa jami’an tsaro sun riga sun isa yankin domin dawo da zaman lafiya da hana sake aukuwar tashin hankali.

Leave a Reply