Sauran Masu Ibada da Aka Sace A Kaduna Sun Shaki Iskar ’Yanci

0 183

An sako sauran mabiya addini da aka sace a yayin harin da aka kai coci uku a Kurmin Wali dake Karamar Hukumar Kajuru, Jihar Kaduna, a ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce a kalla mabiya addini 177 aka sace a harin da aka tsara, inda kusan 80 suka tsira yayin da ake kai su cikin daji, suka sami mafaka a ƙauyukan makwabta.

Shugaban Kurmin Wali, Ishaku Dan’azumi, ya tabbatar da sako mabiya addinin a wata hira ta wayar tarho da PUNCH Online a ranar Alhamis, yana mai cewa yanzu suna tare da gwamnatin jihar Kaduna, amma bai bayar da ƙarin bayani ba.

Shugaban Christian Association of Nigeria (CAN), reshen Kaduna Rev. Ma’aji Caleb, ya ce sako mabiya addinin ya tabbata ne saboda addu’a da kuma kokarin gwamnati, yana mai yabon gwamnan jihar, Uba Sani, saboda jajircewarsa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Wani jami’in ‘yan sanda, wanda ya yi magana ba tare da bayyana sunansa ba, ya tabbatar da sakin su a daren Laraba.

Harin ya sake janyo hankali kan matsalar ‘yan bindiga a Kudancin Kaduna, musamman a karkara inda al’umma ke korafi kan rashin wadataccen tsaro, duk da gudunmawar rundunonin soja da ‘yan sanda a yankin.

Leave a Reply