Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation HADIN KAI sun kama wani da ake zargi da samar da tallafawa ‘yan ta’addan ISWAP, tare da taimaka wa ‘yan Najeriya kusan 700 da suka tsere zuwa Kamaru su dawo gida lafiya a Jihar Borno.
Wata majiya mai tushe a rundunar soji ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a ranar Alhamis a Abuja, cewa an samu nasarar kammala zagaye na biyu na shirin dawo da ‘yan gudun hijira daga Kamaru.
Majiyar ta ce an gudanar da shirin ne a kan iyakar Banki, da ke Karamar Hukumar Bama, inda dakarun Bataliyar Task Force ta 152 tare da sauran hukumomin tsaro suka tabbatar da tsaro.
Rahotanni sun ce ‘yan gudun hijirar kusan 700 sun iso kan iyaka a ranar 31 ga Janairu, sannan aka sake tsugunar da su a garin Banki bisa tsarin haɗin gwiwar tsaro da na jin ƙai.
Gwamnatin Tarayya ta samar da kayayyakin agaji, ciki har da tabarma da tallafin masauki, ta hannun Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Ƙasa, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, UNHCR, yayin da Gwamnatin Jihar Borno ta taimaka wajen rabon kayan.
A wani samame daban, rundunar soji ta kama wani da ake zargi da samar da kayan aiki ga ‘yan ta’addan ISWAP da JAS a ƙauyen Jakana da ke Karamar Hukumar Konduga, inda ake ci gaba da yi masa tambayoyi a hannun soji.
Kazalika, dakarun Battle Group IV sun gano kekuna biyu, buhunan wayoyin lantarki da aka lalata da kuma sandunan ƙarfe a yankin Mulumkoloye na Konduga, waɗanda ake zargin masu laifi ne suka yasar bayan ganin sojoji.