Gomnatin Tarayya Na Fuskantar Suka Bayan Mutane Fiye da 100 sun Mutu A Hare Haren Kwara da Benue

0 165

Fiye da mutane 100 ake fargabar sun mutu sakamakon wani mummunan hari da aka kai wa al’ummomin Woro da Nuku a Karamar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, yayin da wasu da dama ma suka rasa rayukansu a wani harin ‘yan bindiga a ƙauyen Abande da ke Karamar Hukumar Kwande ta Jihar Benue.

Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya tabbatar da mutuwar mutane 75, yana mai cewa an kashe su ne saboda sun ƙi amincewa da koyarwar wasu masu tsattsauran ra’ayi da ke wa’azin wani addini da bai dace da al’ummar yankin ba.

Gwamnan ya ce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da tura bataliyar sojoji zuwa yankin nan take, domin kaddamar da wani farmaki na musamman da aka sanya wa suna Operation Savannah Shield don murkushe ‘yan ta’addan.

‘Yan majalisa da wakilan yankin sun ce lamarin na da rikitarwa, inda rahotanni daga al’umma ke nuna cewa adadin na iya haura wanda gwamnati ta bayyana, tare da rahoton binne mutane kusan 70 a kabari guda a Woro.

Mazauna yankin sun ce maharan sun fito ne daga dazukan yankin kan iyakar Nijar, suna zagayawa suna wa’azi da kira ga barin kundin tsarin mulkin Najeriya, lamarin da ya haddasa rikici bayan wasu mazauna sun kalubalanci su.

Wanda suka tsira daga harin sun bayyana abubuwan tausayi, ciki har da kisan yara da sace mata, yayin da wasu suka tsira ta hanyar tserewa ko hawa bishiyoyi domin gujewa harbin bindiga.

Harin ya sake jefa hankalin jama’a kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, inda jam’iyyun siyasa da tsofaffin shugabanni ke kira ga gaggawar tsoma bakin gwamnatin tarayya, tare da bukatar karin sojoji, agaji da tsauraran matakan kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Leave a Reply