‘Yan Sandan Filin Jirgin SamaN Lagos Sun Kama Wani Matashi Kan Zargin Damfarar N48.5m Ta Kafafen Sada Zumunta

0 210

Rundunar ‘yan sandan filin jirgin sama ta Lagos ta ce ta kama wani matashi ɗan shekara 24 da ake zargi da hannu a wata babbar damfara da ta kai kimanin naira miliyan 48 da dubu dari biyar, kwatankwacin dalar Amurka dubu 35.

Rundunar ta bayyana cewa kamen na daga cikin ci gaba da ƙoƙarinta na hana masu aikata laifuka amfani da harkokin sufurin jiragen sama wajen aikata miyagun ayyuka.

Mai magana da yawun rundunar, ASP Mohammed Adeola, ya ce sashen yaƙi da damfara ne ya kama wanda ake zargin a ranar 2 ga Fabrairu 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka kai ga cafke shi.

An bayyana sunan wanda aka kama da Precious Onudhona, ɗan asalin Jihar Delta, inda aka ce an cafke shi a filin jirgin sama yayin da yake shirin hawa jirgi zuwa Asaba.

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya shiga harkar damfara ne tun shekarar 2023, bayan haɗa kai da wata ƙungiya da ke damfarar mutane ta hanyar soyayya a kafafen sada zumunta kamar Facebook da Instagram.

‘Yan sanda sun ce yana amfani da sunan ƙarya “Travis Kevin”, yana bayyana kansa a matsayin likitan Amurka, tare da ƙirƙirar shafin banki na bogi domin nuna asusun kuɗi na ƙarya, inda yake neman kuɗi da sunan buƙatar magani da abinci bayan samun rauni.

Kwamishiniyar ‘yan sandan filin jirgin sama, CP Ogunbode Olufunke, ta bayar da umarnin zurfafa bincike domin kamo sauran mambobin ƙungiyar, tare da jaddada cewa za a mika wanda ake zargin zuwa sashen Interpol domin ci gaba da bincike da gurfanarwa a gaban kotu.

Leave a Reply