An fara gudanar da gangamin fadakar da al’umma hanyoyin dakile cutar kwalara a kananan hukumomi 10 na jihar Jigawa

0 85

Kwamatin Dakile Cutar Kwalara a Kananan Hukumomin Jihar Jigawa tare da hadin gwiwar shirin Save the Children International sun fara gudanar da gangamin fadakar da Al’umma kan hanyoyin dakile cutar a Kananan Hukumomi 10 na Jihar nan.

Shugaban Kwamatin na Karamar hukumar Birnin Kudu, Malam Bello Abdulkareem, shine ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce kimanin Magidanta dubu 1000 ne aka basu kayayyakin kariya daga cutar a Kananan Hukumomi 10 na Jigawa.

A cewarsa, Kungiyar Save the Children International ce take samarwa gwamnatin Jihar Jigawa tallafi domin yaki da cutar Kwalara.

Haka kuma ya ce ana gudanar da gangamin yaki da cutar a Kananan Hukumomi 10 wanda suka hada da Dutse, Ringim, Jahun, Garki, B/Kudu, Gwaram, Guri, M/Madori, Hadejia da kuma Buji.

Kazalika, ya ce an bawa Mutane 150 horo daga Mazabu 30 kan yadda zasu dakile bullar cutar a Kananan Hukumomi 10 wanda cutar ta fi yiwa illa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: