Yadda aka sace wata yarinya mai shekaru 5 a unguwar Kawaji dake birnin Kano

0 104

An sace wata yarinyar mai shekaru 5, mai suna Hanifa Abubakar, a unguwar Kawaji dake birnin Kano.

Masu sace mutane ne suka yi awon gaba da ita, lokacin da suka zo akan keke napep suka yaudareta akan zasu dana ta.

An rawaito cewa lamarin ya auku da misalin karfe 5 na yamma, yayin da yarinyar tare da sauran yaran makota ke dawowa daga makarantar Islamiyya.

Kamar yadda yazo ta bakin wasu yaran da suka shaida lamarin, masu satar mutanen sun zo akan keke napep kuma suka nemi rage musu hanya zuwa gida. Bayan sun ajiye su, sai suka ce Hanifa ta sake hawa domin dana ta, daga nan suka wuce da ita.

Unguwar Kawaji dake karamar hukumar Nasarawa, na daya daga cikin unguwannin da ake yawaitar samun satar yara a Kano.

A unguwar aka sace wani yaro dan shekara 9 mai suna Yusuf Nasiru, a ranar 28 ga watan Disambar bara, bayan ya dawo daga makarantar Islamiyya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: