An fara zaman shari’ar tsohon shugaban Burkina Faso, Blaise Compaore

0 187

An tuhumi Blaise Compaore tsohon shugaban kasar Burkina Faso a bayan idonsa saboda kisan magabacinsa Marigayi Thomas Sankara yayin wani juyin mulki fiye da shekaru 30 da suka gabata.

Kotu a kasar Burkina Faso ta tuhumi tsohon shugaban kasar Blaise Compaore a bayan idonsa bisa zargin kan kisan magabacinsa tsohon Shugaba Thomas Sankara a wani juyin mulkin shekarar 1987.

An tura shari’a wata kotun soja da ke birnin Ouagadougou fadar gwamnatin kasar inda ake tuhumar Compaore da wasu mutane da hannu wajen kisan na kimanin shekaru 34 da suka gabata.

Shi dai Blaise Compaore dan shekaru 70 da haihuwa yanzu hana yana zama a kasar Cote d’Ivoire, tun lokacin da boren jama’a ya kawo karshen gwamnatinsa a shekara ta 2014, bayan mulkin kimanin shekaru 27. Lauyan Marigayi Thomas Sankara tsohon shugaban wanda aka kashe lokacin juyin mulkin ya tabbatar da zaman fara shari’ar gano wadanda suke da alhakin kashe Sankara wanda ya yi suna lokacin da yake rike da madafun ikon kasar ta Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka.

Hakkin mallaka; VOAHausa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: