Dalibai 20 A Wata Makarantar Firamarin Yamai Sun Mutu A Dalilin Barkewar Mummunar Gobara.

0 84

Gobarar da ta tashi a wata makarantar firamarin birnin Yamai ta haddasa rasuwar dalibai da dama yayinda baki dayan dakanun karatu suka kone kurmus.

Lamarin ya sa hukumomin ilimi a matakin jihar suka rufe makarantu a tsawon wunin laraba 14 ga watan maris domin nuna juyayin faruwar wannan al’amari da har yanzu ba a san tushensa ba.
Lamarin ya faru ne bayan karfe 4 na la’asariyar talata a dai dai lokacin da daruruwan dalibai ke daukar karatu a wata makarantar frimarin n’guwar Pays Bas mai dakunan karatu kusan 30 dukkansu na zana.

Fira minister Ouhoumoudou Mahamadou tare da maya bayan ministan ilimi Dr Rabiou Ousman da na cikin gida Alkache Alhada da gwamnan yamai Oudou Ambouka sun ziyarci makarantar da wannan mumunan iftila’I ya afkawa jim kadan bayan jami’an kwana kwana sun kashe wannan gobara.

Fira ministan ya ce “mun zo ne don mu jajantawa jama’a faruwar wannan abin bakin ciki domin yaran da abin ya rutsa da su ‘yayanmu mu duka kuma zamu gudanar da bincike domin gano tushen wannan gobara”.

Karantar da yara a dakunan karatun da aka yi su da darni ko zana wata dadaddiyar matsala ce da dalibai da malaman makaranta suka sha korafi akanta saboda la’akari da hadarin da take tattare da shi. Sabon shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum a jawabinsa na rantsuwar kama aiki ya sha alwashin dakatar da karantarwa a irin wannan dakuna da ake kira classe paillote a faransance.

Asalin labarin;

VOAHAUSA

Leave a Reply

%d bloggers like this: