Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace annobar corona ta bankado damarmaki da hazaka da kuma basirar masana kimiyyar kasarnan.

A wani jawabi da ya gabatar a wajen wani taro wanda makarantar injiniyanci ta Najeriya ta shirya, shugaban kasar ya yabawa injiniyoyin Najeriya bisa gogewarsu da kwarewarsu.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Yemi Osinbajo, ya yabawar makarantar tare da dalibanta.

Da yake magana akan muhimmancin kimiyya, fasaha da injiniyanci wajen magance annobar Corona, shugaban kasar yayi nuni da cewa duniya ta koma irin wannan ilimomin domin samun hanyoyin warware matsaloli cikin gaggawa.

Shugaban kasar yayi tuni da dokarsa ta zartawa mai numba ta 5 wacce ta umarci dukkan ma’aikatu da sassa da hukumomin gwamnati da suke hada kai da kwararrun masana yan kasa wajen tsare-tsare, da aiwatar da dukkan ayyukan tsaron kasa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: