Karshen Tika-Tika Tik, Ahmed Musa Ya Koma Kano Pillars.

0 126

Bayan ya shafe shekaru 10 da barin Kungiyyar Musa ya dawo Kano Pillars.

Masu iya magana na cewa ta faru ta ƙare an yiwa mai dami ɗaya sata biyo bayan maganganun da suke ta zagaye a dandalin sada zumunta dangane da komawar Ahmad Musa zuwa tsohuwar ƙungiyarsa ta Kano Pillars.

A yammacin jiya dai maganar ta tabbata inda takarda ta fito daga ofishin Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Kano Pillars wato Alhaji Surajo Sha’aibu Yahaya Jambul wanda shi ne mai magana da yawun ƙungiyar, inda ya bayyana cewa Ahmed Musa ya rattaɓa a Kungiyyar.

A shekarun baya dai Ahmad Musa ya bugawa Kano Pillars wasanni sosai inda daga lokacin kuma ya koma nahiyar Turai da fafata wasan nasa.
Idan zamu tunawa dai a kakar wasanni ta 2009-10, Ahmed Musa ya zuwa Kano Pillars Kwallaye 18 a firimiyyar Nijeriya wanda har kawo yanzu babu ɗan wasan da ya taɓa zura sama da yawan Kwallayen nasa.

Ahmad Musa dai ya kwashe watanni ba tare da yana fafata wasa ba biyo bayan yadda tsohuwar ƙungiyarsa ta Saudiyya Al-nasr tacemasa lokaci yayi da zai tafi wata ƙungiyar.

Hakan na nufin Ahmad Musa zai bugawa Kano Pillars ragowar wasanninta na gasar ajin kwararru na NPFL wanda yanzu aka juya dan buga ragowar wasanni 19.

Daga yanzu zuwa kowanne lokaci gwamnan jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai iya gabatar da Ahmad Musa a matsayinsa na sabon ɗan wasan Kano Pillars.

Daga ƙarshe Malikawa ya bayyana cewar dukkanin iyalan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars na yin maraba da dawowar Ahmad Musa zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars.

Leave a Reply

%d bloggers like this: