An goge hotunan mata da ke kan allon talla a cikin birnin na Kabul na kasar Afghanistan

0 86

Kwanaki biyu bayan kwace Kabul fadar gwamnatin Afghanistan, kungiyar Taliban ya sanar da yin afuwa ga jami’an gwamnati, tare dayin kira gare su da su koma bakin aiki.

A filin jirgin sama na Kabul, jirage sun cigaba da kwashe sojoji da jami’an diflomasiyya da sauran fararen hula.

An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a jiya lokacin da dimbin mutanen da ke cikin mawuyacin hali suka yi kokarin shiga jirage don tserewa daga birnin na Kabul.

Wakilin BBC ya ce tituna sun kasance fayau kuma an rufe shaguna da dama a Kabul.

Kazalika babu kidan da aka saba a gidajen abinci da motoci kuma mata kalilan ne ake gani akan titi.

Tuni aka goge hotunan mata da ke kan allon talla a cikin birnin na Kabul.

Leave a Reply

%d bloggers like this: