Wasu ‘yan fashi da makami sun kashe akalla mutane hudu a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina

0 87

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kashe akalla mutane hudu, jiya a kauyen Tsayau da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Dan majalisar mai wakiltar Jibia a majalisar dokokin jihar, Mustapha Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ya ce ‘yan bindigar sun tafi tare da mutane da dama inda suka raunata wasu mutane 7 bayan harin da aka kai kan manoma.

Majiyoyin yankin sun kuma shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun afkawa kauyen ne da misalin karfe 7 da minti 50 na dare, dauke da manyan makamai, inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane hudu.

Bayanai sun kara da cewa jami’an tsaro sun isa kauyen bayan maharan sun gudu tare da mutane da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: