Kasar Uganda za ta karbi ‘yan gudun hijirar Afghanistan su dubu 2 da suka tserewa rikicin kasarsu

0 128

Kasar Uganda za ta karbi ‘yan gudun hijirar Afghanistan su dubu 2 da suka tserewa rikicin kasarsu.

Ministar kula da ‘yan gudun hijira Esther Anyakun ta shaidawa manema labarai cewa shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni ya amince ya karbi ‘yan gudun hijirar bisa bukatar gwamnatin kasar Amurka.

Hakan ya biyo bayan mamayar ‘yan Taliban a karshen mako, da rushewar gwamnatin Afghanistan ta Ashraf Ghani.

Ana sa ran rukunin farko na ‘yan Afghanistan kusan 500 za su sauka a filin jirgin saman Entebbe a kasar Uganda nan da sa’o’i kalilan.

Ministar ta kara da cewa za a yiwa wadanda suka iso gwajin corona kuma a killace su. Gwamnatin Amurka ce za ta kula da duk abubuwan da za’a bukata.

Idan suka sauka, Uganda za ta zama kasar Afirka ta farko da za ta karbi mutanen da ke tserewa rikicin Afghanistan na yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: