An Hana Wasu Dalibai Yan Najeriya Dake Kokarin Tserewa Rikicin Sudan Shiga Kasar Habasha

0 75

Gwamnatin tarayya a jiya ta tabbatar da cewa wasu dalibai ‘yan Najeriya dake tserewa rikicin da ake yi a Sudan, an hana su shigar kasar Habasha amma ta bayyana cewa ana kokarin warware matsalar.

Gwamnatin tace hukumomin Najeriya a kasar Habasha na kokarin warware matsalar, kasancewar sun nemi takardar izinin barin daliban shiga kasar, sai dai ta jaddada cewa abu ne mai hatsari ga daliban da suka yi wannan tafiyar.

A halin da ake ciki kuma, wata kungiya ta ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, a jiya ta nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta kwaso ‘yan Najeriya dake zauna a kasar Sudan wacce yaki ya Daidaita.

Shugaban kungiyar, James Erebuoye, shine yayi kiran cikin wata sanarwa da ya fitar. Ya kuma soki halin matsin tattalin arzikin da ake ciki a Najeriya, inda yace da komai yana tafiya yadda ya kamata a kasarnan, ‘yan Najeriya baza suke tafiya wasu kasashen ba da nufin samun kyakykyawar rayuwa ko neman ilimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: