Mutum 5 Sun Mutu A Wani Hatsari Da Ya Afku A Kan Hanyar Bauchi Zuwa Jos

0 85

Hukumar kiyaye hadurra ta tarayya a jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane biyar tare da wani mutum daya da ya samu rauni a wani hatsarin mota daya tilo da ya afku jiya a Tashan Durumi dake kan hanyar Bauchi zuwa Jos.

Kwamandan hukumar a jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce hatsarin ya shafi wata motae haya ce kirar Astra Vectra da ke gudun da ya wuce hankali a wanda ake kyautata zaton shine musabbabin hatsarin.

Ya bayyana cewa mutane biyar sun mutu, wadanda suka kunshi namiji babba daya da manyan mata hudu.

A wani labarin kuma, ruwa ya mamaye gidaje da dama bayan anyi ruwan sama kamar da bakin kwarya a garin Jalingo na jihar Taraba da safiyar jiya.

Lamarin dai ya faru ne a lokacin da kogin Mayo Gwoi ya cika ya tumbatsa bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwashe kusan sa’o’i biyu ana yi.

Duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, amma ambaliyar ta lalata dukiyoyi da suka hada da kayan gida da kayan abinci na miliyoyin naira.

Leave a Reply

%d bloggers like this: