Peter Obi A Jiya Ya Yi Bikin Sallah Karama Da Al’ummar Musulmi A Jihar Anambra

0 50

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, a jiya ya yi bikin Sallah karama da al’ummar Musulmi a Awka, babban birnin jihar Anambra.

Peter Obi, wanda ya bayar da gudummawar kayan abinci da suka hada da buhunan shinkafa, da katanan na taliya, da lemukan sha, da tsabar kudi, ya ce kamata yayi addini ya hada kan ‘yan Najeriya, ba wai ya raba su ba.

Ya ce kowane dan Adam daidai yake a wajen ubangiji inda yayi nadamar yadda wasu ‘yan siyasa suke amfani da banbancin addini domin amfanin kansu da kuma cutar da al’umma.

Peter Obi ya godewa al’ummar Musulmin Awka da suka gayyace shi zuwa bikin Sallah yayin da ya yi alkawarin taimakawa wajen kammala aikin babban masallacin Juma’a na Awka. Da suke mayar da martani, shugabannin al’ummar Arewa mazauna Awka, da kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah da kuma majalisar koli ta harkokin addinin Musulunchi a Awka, sun yabawa Peter Obi bisa kyakkyawar alaka da suka yi da gwamnatinsa lokacin da yake gwamna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: