An kama mutanen da suka kai gurbatacciyar masara jihar Kano

0 107

Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, ta kama mutane 2 bisa zargin su da hannu a kayan laifukan da hukumar ta kama na wasu Manyan Motoci dauke da Gurbatacciyar Masara a Kasuwar Dawanau.

Mukaddashin Shugaban Hukumar Barrister Mahmoud Balarabe, shine ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan sun killace wurin da kayan suke.

A cewarsa, hukumar ta samu masaniyar sirri kan cewa wasu mutane sun boye gurbatacciyar Masara a Kasuwar Dawanau din.

Haka kuma ya ce daga cikin abubuwan da hukumar ta kama sun hada da Tirela 1 na gurbatacciyar Masarar, da kuma Buhu 10 na Gero.

Mukaddashin Shugaban Hukumar, ya ce kaso 90 na Masarar ya lalace, kaso 10 ne kadai za’a iya amfana, kuma ana kokarin fita da ita zuwa wani Kamfani domin sarrafawa.

Barista Balarabe, ya bukaci Al’umma su tallafawa kokarin hukumar dana gwamnati domin ganin cewa sun kai ga Nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: