Majalisar Karamar Hukumar Hadejia ta fara feshin maganin sauro a cikin garin Hadejia

0 107

Majalisar Karamar Hukumar Hadejia ta fara feshin Maganin Sauro a wani mataki na korar Sauron a fadin garin na Hadejia.

Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Abdulkadir Bala Umar T.O, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Karamar Hukumar Muhammad Garba Talaki, ya rabawa manema labarai a Dutse.

A cewarsa, shugaban Karamar karamar ya ce aikin zai zagaya Mazabu 11 na karamar hukumar Hadejia domin dakile zazzabin cizon sauro wand yake cigaba da yaduwa.

Alhaji Bala Umar T.O ya bukaci Kungiyoyin su tabbatar da cewa sun yashe magudanan ruwan su.

Sanarwar ta labarto wurin da Shugaban Sashen Ruwa da Tsaftar Muhalli Alhaji Muhammad Abdullahi, ya ke cewa Majalisar ta samar da ma’aikatan da zasu yi aikin da kuma dukkan kayan aikin da ake bukata domin gudanar da aikin kamar yadda ya kamata.

Kazalika, Shugaban Sashen na WASH ya ce Majalisar karamar hukumar tana kokarin ganin cewa ta kirkiri yin feshin duk wata domin korar zazzabin cizon Sauron gaba daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: