Gwamnatin jihar Jigawa ta fara gabatar da sabbin shirye-shiryen koyan karatu ta hanyar rediyo

0 145

Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara gabatar da sabbin shirye-shiryen ga magidanta maza da mata domin koyan karatu ta hanyar radio.

A jawabinsa Sakataren zartarwa na hukumar Ilimin Manya na Jihar Jigawa Dr Abbas Abubakar Abbas ya ce magidanta dubu 1,000 ne zasu sami akwatinan radion domin koyan karatu ta hanyar radio.

Dr Abbas A Abbas ya kara da cewar hakan na daga cikin manufar gwamnatin jiha na bunkasa ilmin manya, inda ya yi fatan magidanta dake cikin shirin zasu rinka bibiyar gidan radion domin koyan karatun a matakin farko.

Yace radion mai amfani da hasken rana zai sawwakawa magidantan wajen sayen batir, inda yace za a rinka tara magidanta ana yi musu tambayoyi kan abubuwan da suka amfana.

Dr Abbas A Abbas ya yabawa gwamna Badaru Abubakar bisa kishi da kulawar da yake yiwa hukumar wajen bunkasa llimin manya a jihar nan.

 Yace  za a raba radion a raguwar kananan hukumomin jihar nan 18 da basa cikin shirin koyan karatu ta radio na gwamnatin tarayya, kuma za’a fara koyar da karatun daga ranar 4 ga watan Octoba zuwa watan Maris na 2022.

Hukumar Ilimin Manya ta Kasa a kwanan nan ta raba Radiyo 307 a Jihar Jigawa domin yaki da Jahilci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: