Daga: A Yawale

Matashin da akayi wa wannan aika aika mai suna Muhammad Usman dan asalin garin Mairakumi ne dake yankin karamar hukumar Mallam Madori a jihar Jigawa.

A hirarsu da wakilin JAKADIYA matashin yace, cacar baki ce ta hada su daga nan sai abokin nasa ya caka masa wuka, da ya ga wukar bata kamashi shi ba sai ya dauko almakashi ya caka masa a ciki.

Yanzu haka dai an garzaya da matashin zuwa asibitin kwanciya na Hadejia inda ake duba lafiyarsa.

Yayin da shi kuma Wanda ake zargin yana can a hannun ‘yansanda domin zurfafa bincike kan lamarin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: