Mutum 780 ne suka yi sauyin sheka zuwa Jam’iyar PDP daga APC a karamar hukumar Kazaure ta nan Jihar Jigawa

0 116

A kalla Yayan Jam’iyar APC 780 ne suka yi sauyin sheka zuwa Jam’iyar PDP a karamar hukumar Kazaure ta nan Jihar Jigawa.

A cewar masu sauyin shekar sun bar Jam’iyar APC ne zuwa PDP biyo bayan tsarin da Jam’iyar take dashi na shugabanci.

Da yake karbar masu sauyin Shekar tsohon Dan Majalisar tarayya Hon Bashir Jimbo Kazaure, ya bukaci yan siyasa su kasance masu jin tsoron Allah a siyasar su.

Shima a Jawabinsa, Shugaban Jam’iyar PDP na Jihar Jigawa Hon Babandi Ibrahim Gumel, ya bayyana APC a matsayin Jam’iyar Yaudara wanda ta jefa yan kasa a cikin rudani.

Hon Babandi Ibrahim, ya lissafo matsalolin rashin tsaro da cin hanci da rashawa da Talauci da kuma rashin ayyukan yi a tsakanin Matasa a matsayin gazawar Jam’iyar APC.

Kazalika ya bukaci masu sauyin shekar su kasance masu Jajircewa a cikin sabuwar Jam’iyar ta su ta PDP.

Leave a Reply

%d bloggers like this: